Syria

Sabon rikici ya barke a birnin Syria

Sabon rikici ya barke a Damascus
Sabon rikici ya barke a Damascus AMER ALMOHIBANY / AFP

An samu barkewar sabon rikici a birnin Damasacus da ke Syria bayan ‘yan tawaye sun kai wani hari na bazata kan dakarun gwamnati Shugaba Assad.

Talla

Harin na zuwa ne kwananki kadan a bude sabon tattaunawar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta a Geneva don kawo karshan zub da jinni a yakin basasar shekaru 6 a kasar.

An jiyo karar harbe-harbe bayan ‘yan tawaye da ke samun goyon bayan Al-qaeda da Fateh al-sham sun kaddamar da hari kan dakarun da ke gabashin birnin Damascus.

Harin ya soma ne da na bama-bamai da aka kai da mota da kuma na kunar bakin wake a yankin Jobar.

‘Yan tawayen sun kwace ikon gine-gine a Jobar da kutsa kai cikin fillin Abbasid, inda suka karbe ikon tashar mota da harba rokoki.

Kungiyar da ke sa’ido kan rikicin Syria, ta ce jiragen yakin kasar sama da 30 sun ta ruwan wuta tun safiya kan ‘yan tawaye.

Wakilin Kamfanin dilanci labaran faransa AFP, ya rawaito cewa dakarun soji sun yiwa ‘yan tawayen kawanya a Damascus

Rikicin na wannan lokaci na zuwa ne bayan amincewar ‘yan tawaye da dakarun gwamnati na tsaigata bude wuta a kasar cikin watan Disamba da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI