Myanmar

Wata ta kai Danta kotu a Myanmar saboda ya kira ta Karuwa

Ministan cikin gidan Myanmar Kyaw Swe
Ministan cikin gidan Myanmar Kyaw Swe REUTERS

Wata Mata a Kudancin Myanmar ta maka danta a kotu bayan ya kira ta da sunan Karuwa tare da yada hutunanta a shafin facebook saboda yana adawa da wani sabon saurayinta.

Talla

A ranar Talata ‘Yan sanda suka cafke yaron mai suna Wana Oo dan shekaru 21 bayan mahaifiyarsa mai suna Tin Tin Hla ta tuhume shi da cin mutuncinta a Facebook.

‘Yan sandan Myanmar sun ce matar ta kai karar yaron a Kotu wanda ya karba laifin da mahaifiyarsa ke tuhumarsa.

Wana Oo zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari karkashin dokar da ta haramta cin mutuncin wani a kafofin sadarwa na zamani.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama  na ganin dokar ta sabawa ‘yancin fadin albarkacin baki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI