Pakistan-India

Pakistan ta tsare masunta 100 'yan kasar India saboda shiga harabar tekun Pakistan.

Yankin tekun Pakistan a wani hoto da aka dauka a shekara ta 2010.
Yankin tekun Pakistan a wani hoto da aka dauka a shekara ta 2010. AFP /JAPAN POOL

Hukumomi a kasar Pakistan na tsare da wasu masunta 100 ‘yan kasar India saboda zargin suna sana’ar ta su a yankunan tekun Pakistan. 

Talla

Majiyoyin samun labarai na cewa Hukumar Kulada da yankunan tekun Pakistan  ta yi wannan kame, da kuma kamen wasu kwale-kwake 19 da aka yi amfani da su.

Duk shekara akan sami irin wannan kame na masunta da ake zargi suna shiga harabar tekun juna.

Koda a watan janairu na wannan shekara sai da Hukumomin Pakistan suka yiwa wasu masunta 219 ‘yan kasar India  da ake tsare da su afuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI