Rasha

An Tsare Madugun Adawa na kasar Rasha saboda shirya zanga-zanga

Madugun adawa a kasar Rasha Alexeï Navalny
Madugun adawa a kasar Rasha Alexeï Navalny REUTERS/Maxim Shemetov

Dubban ‘yan kasar Rasha ne  yau lahadi suka gudanar da zanga-zanga don nuna kyamar cin hanci da rashawa, inda suka bijirewa umarnin da Hukumomin kasar suka bayar  cewa kada a kuskura ayi zanga-zangan, wanda madugun adawa Alexei Navalny ya kira.

Talla

Shi dai madugun adawan ya kira zanga-zangan ne bayan da aka wallafa wasu bayanan sirri dake nuna Firaminista Dmitry Medvedev ya mallaki wasu tulin dukiya da sunan wani nasa.

Ma'abuta shafin sadarwa na Youtube sama da mutane miliyan 11 suka shiga shafin da aka bankado zargin da ake yiwa Firaministan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.