Hong Kong

Mai ra'ayin China ta lashe zaben Hong Kong

Carrie Lam sabuwar shugabar Hong Kong
Carrie Lam sabuwar shugabar Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu

A Hong Kong an zabi Carrie Lam a matsayin sabuwar shugaba bayan kwamitin da ke goyon bayan China sun kada kuri’ar a yau Lahadi. Zaben da ya fuskanci suka daga ‘yan kasar da suke son a ba kowa yancin kada kuri’a, maimakon wasu tsiraru.

Talla

Tun kafin kada kuri’a aka yi has ashen Carrie Lam mataimakiya ga shugaban Hong Kong da China ke ra’ayi za a zaba.

Kwamitin zaben ya kunshi mambobi 1,194, kuma Lam ta lashe zaben ne da yawan kuri’u 777.

A watan Juli ne Lam za ta karbi jagoranci daga Leung da ya shafe shekaru 5 yana shugabanci.

Hong Kong dai kasa ce amma mai bin tsari biyu, bayan ta koma ikon China daga Birtaniya a 1997, shekaru 20 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.