Bakonmu a Yau

Bukatar 'yan Najeriya, ya dace Shugaba Buhari ya aiwatar da sabon tsari

Sauti 03:33
Tutar Tarrayar Najeriya
Tutar Tarrayar Najeriya

A Najeriya bayan da manyan jami’an Gwamnatin kasar ke karo da juna wajen aiwatar da manufofin gwamnati da kuma yiwa kasa aiki, ya sa wasu yan kasar bukatar ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi garambawul dan kawo wadanda zasu taimaka masa sauke alkawarin da ya yi wa talakawa.

Talla

Wannan ya biyo bayan zargin zagon kasa da ake yi wa wasu manyan jami’an gwamnati dake hana ruwa gudu wajen tafiyar da aikin shugaban kasar.

Mun tattauna da Hajiya Naja’atu Muhammad, daya daga cikin jiga jigan Jam’iyyar APC kuma ga tsokacin da tayi mana a kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.