Syria-Amurka

Amurka ta lashi takobin sake kai harin makami mai linzami Syria

Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Shugaban kasar Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque

Kasar Amurka ta lashi takobin sake kai hare-haren makami mai linzami Syria, domin zama darasi ga wadanda ake zargi da hannu wajen amfani da makami mai guba wajen kai hare-haren da ya lakume rayuka 86 a farkon wannan makon.

Talla

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikky Haley da ke tabbatar da gaban-kan-ta da kasar ke yi ta ce a shirye suke domin sake yin amfani da karfin soji idan akwai bukatar yin haka.

Shugaba Donald Trump shi ma a jawabansa ya jadada matsayinsu inda ya ce ba zai raga a Syria ba muddin aka ci gaba da amfani da irin wannan makami kan fararen hula.

Masu sharhin kan lamuran duniya, na furgaban sake rincebewar rikicin Syria muddin manyan kasashen da ke yaki a kasar suka gagagara cim-ma dai-daito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.