Syria

Ana kwashe fararen hular da aka yi wa kawanya

An soma aikin  kwashe fararen hular da aka yi wa kawanya a Syria.
An soma aikin kwashe fararen hular da aka yi wa kawanya a Syria. REUTERS/Ammar Abdullah

An fara aikin kwashe daruruwan fararen hula daga garuruwa hudu da aka yi wa kawanya tsawon shekaru biyu a Syria, bayan cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakanin gwamnatin kasar da kuma ‘Yan tawaye da ke yaki da juna.

Talla

Ana kwashe fararen hular da aka yi wa kawanya a garuruwa biyu wato Foah da Kefraya yankunan da dakarun gwamnatin Syria ta kwace daga hannun ‘Yan tawaye.
Haka ma ana kwashe fararen hula a yankin Madaya da Zabadani da ke karkashin ikon ‘Yan tawaye.

Rahotanni sun ce kimanin motoci 80 suka kwashe fararen hular daga garuruwan Fouah da Keraya da ke lardin Idlib arewa maso yammacin Syria.

Kuma kimanin fararen hula dubu talatin ake fatar kwashewa daga yankunan guda hudu da aka yi kawanya tsawon shekaru biyu ana yaki a yankunan da ke kusa da Aleppo.
Tun a 4 ga watan Afrilu ya kamata a soma aikin kwashe mutanen karkashin yarjejeniyar da Qatar da Iran suka jagoranta.

Amma matakin ya gagara saboda rashin bayar da goyon bayan bangarorin da ke rikici a Syria.
Yawancin dai wadanda aka kwashe mata ne da yara kanana wadanda rahotanni suka ce sun isa yankin Rashidin wadanda aka kwaso daga yankunan da ke ikon ‘yan tawaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.