Syria

Sojojin Syria za su tsagaita buda wuta-Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Sputnik/Alexei Druzhinin/Kremlin via REUTERS

Gwamnatin Rasha ta ce Sojojin Syria sun amince su tsagaita buda wuta domin gudanar da binciken hare haren makami mai guba da aka kai a yankunan da ke karkashin ikon ‘Yan tawaye.

Talla

Sai dai babu wani tabbaci daga bangaren gwamnatin Syria dangane da ikirarin da Rasha ta yi.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta fadi ne a cikin wata sanarwa cewa dakarun Syria a shirye suke su tsagaita buda wuta domin ba kwararru na MDD damar gudanar da binciken harin makami mai guba da aka kai a yankunan da ‘yan tawaye ke iko a ranar 4 ga Afrilu.

Sannan sanarwar ta kara cewa Syria ta yi alkawarin dakatar da ayyukan dakarunta na wucci gadi a yankin Idlib da aka kai harin domin gudanar da binciken.

Harin dai ya salwantar da rayukan mutane 87 da suka hada da mata da yara kanana, kuma Gwamnatin Syria ce ake zargi da kai harin.

Rasha kuma ta dade tana kare gwamnatin Bashar Assad akan amfani da makami mai guba kan ‘yan tawaye.

Sai dai kuma gwamnatin Syria a yanzu ba ta fito ta tabbatar da ikirarin na Rasha ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.