Yemen

Yemen: Ana bukatar dala biliyan 2 don ceto mutane miliyan 17 daga yunwa

Wata mata dauke da jaririnta a sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da birnin Sanaa a kasar Yemen
Wata mata dauke da jaririnta a sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da birnin Sanaa a kasar Yemen REUTERS/Khaled Abdullah

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ‘yan kasar Yemen 17 zasu a cikin masifar tsananin yunwa muddin kasashe basu taimaka wajen kare aukuwar hakan ba.

Talla

Sakataren majalisar Antonio Guterres ne yayi wannan gargadi yayinda ya jagoranci kaddamar da gidauniyar taimakawa la’ummar kasar Yemen a birnin Geneva.

Yayin taron kasashen duniya sun yi alkawarin taimakawa kasar da kudaden da suka zarce Dala biliyan guda domin magance matsalar karancin abinci, al’amarin da ya haifar da matsananciyar yunwa ga milyoyin ‘yan kasar.

Ministan harkokin wajen Switzerland Didier Burkhalter wanda ya jagoranci taron da takwaransa na kasar Sweden yace abin takaici ne ganin an zuba ido ana kallon yadda yunwa ke hallaka al’umma a kasar ta Yemen.

Rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa sama da kananan yara miliyan 2 na fama da yunwa a yemen, lamarin da yasa majalisar yin hasashen akalla yaro daya ne ke rasa ransa a duk bayan mintuna 10 a kasar, sakamakon rashin abinci.

Kasar Yemen dai na cikin kasashen da ke fama da talauci, to sai dai yakin da ake gwabzawa tsakanin mayakan Houthi da sojin gwamnati da ke samun goyon bayan kasar Saudiyya, ya kara munin yanayin da kasar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.