Isa ga babban shafi
India

Jarumin Fim din India Vinod Khanna ya rasu

Jarumin Fim a India Vinod Khanna
Jarumin Fim a India Vinod Khanna thereel
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Daya daga cikin jaruman finafinan India a masana’antar Bollywood Vinod Khanna ya rasu yana da shekaru 70 a duniya bayan ya yi fama da cutar kansa.

Talla

Vinnod Khanna ya fara shirin fim na India a shekarar 1968 kuma Fim din sa na farko dai shi ne Man Ka Meet, amma an fi tuna shi a “Mera Gaon Mera Desh” da “Achanak” da kuma “Amar Akbar Anthony” da suka yi da Amitabh Bachchan da Rishi Kapoor.

Ya kuma shiga siyasa inda ya zama Dan majalisa a Jihar Punjab.

Khanna ya karbi kyautuka da dama a rayuwarsa ta fim a India. Fim na karshe da ya fito shi ne Dilwale a shekarar 2015.

Rasuwarsa ta girgiza Jaruma fim din India da dama, duk da ya shafe lokaci yana jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.