Syria

HRW ta zargi Syria da amfani da makami mai guba

HRW ta zargi Syria da Amfani da Makami mai guba a yakin da ta ke yi
HRW ta zargi Syria da Amfani da Makami mai guba a yakin da ta ke yi REUTERS/Ammar Abdullah

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi dakarun gwamnatin Syria da yin amfani da makami mai guba a cikin wasu hare hare hudu na kwana kwanan nan da aka kai a garin khan Sheikun.

Talla

Kungiyar ta bayyana hare haren a matsayin cin zarafin bil’adama. Rahoton ya yi nuni da cewa dakarun gwamnatin Syria na amfani da makami mai guba na chlorine wajen harba makamin mai linzami a yakin da ake gabzawa kusa da birnin Damascus.

A cewar babban daraktan kungiyar, Kenneth Roth, cikin watanni shidda, gwamnatin Bashar al- Assad ta yi amfani da jiragen yaki, da jirage masu saukar angulu da kuma hanyoyi na kasa wajen kai wa dakarun gwamnatin makami mai guba na Chlorine da Sarin a garurukkan Damascus da Hama da Idlib da kuma Aleppo.

Human Rights watch ta ce ta samo wadan nan bayanai ne, sakamakon hirarraki da ta yi da wasu shedu, mutane 60, da kuma hotunan bidiyo da ke nuna yadda aka yi amfani da makami mai linzami wajen kai harin a garin khan sheikun a ranar 4 ga watan Afirilu.

Kana akwai wasu hare haren uku da ake zargin anyi amfani da makami mai guba a watan Disambar 2016 da kuma watan Maris din wannan shekara.

Akalla mutane 92 ne dai ake zargin makami mai gubar ya kashe ciki kuwa hadda kananan yara guda 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.