Syria

‘Yan tawayen Syria sun janye daga Zaman sulhu

Tattaunawar Zaman lafiyar Syria a Astana
Tattaunawar Zaman lafiyar Syria a Astana Reuters/Mukhtar Kholdorbekov

‘Yan tawayen Syria sun sanar da janyewa daga zaman tattaunawar sasanta rikicin kasar da aka soma karo na hudu a birnin Astana na Kazakhstan saboda rashin tsagaita buda wuta daga bangaren gwamnati.

Talla

Wannan na zuwa a yayin da Rasha ke shirin gabatar da kudirin hana shawagin jirage domin dorewar tattaunawasar sasanta rikicin Syria.

‘Yan tawayen sun ce za su ci gaba da kauracewa zauren tattaunawar har sai an dakatar da kai hari a fadin Syria.

A jiya ne dai aka bude zuuren tattaunawar karo na hudu tsakanin wakilan gwamnatin Bashar al Assad da kuma ‘yan tawaye.

Rasha da Iran da ke marawa Assad baya ne ke jagorantar tattaunawar da kuma Turkiya da ke goyon bayan ‘Yan tawaye.

Akwai dai kudirin da Rasha ta tsara da ta ke bukatar bangarorin biyu su amince domin samun dorewar tattaunawar da za ta kawo karshen yaki a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.