Qatar- Saudiya

Kasashen larabawa sun gaza cim ma daidaituwa da Qatar

Kasashen Yankin tekun fasha sun gaza cim ma daidaituwa da Qatar
Kasashen Yankin tekun fasha sun gaza cim ma daidaituwa da Qatar BANDAR AL-JALOUD / Saudi Royal Palace / AFP

Kasashen yankin Gulf da suka yanke huldar Diflomasiyya da kasuwanci da Qatar sun ce matakan da suka dauka kan kasar na nan daram sakamakon gaza cim-ma wasu sharudan da suka gindaya mata.

Talla

Kasashen sun bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ministocin harkokin wajen kasashen suka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar.

Tattaunawar na zuwa ne wata guda bayan kasashen na larabawa hudu sun amince da yanke dukkanin huldar jakadanci da Qatar sakamakon zarginta da marawa ta’addanci baya.

Daga cikin bukatun da kasashen hudu suka mikawa kasar ta Qatar a matsayin sharuddan sake dawowarta cikin kungiyarsu akwai kawo karshen mara baya ga kungiyar ‘yan uwa Muslmi da ke masar da kuma rufe tashar Aljazeera.

Sauran bukatun sun hada da yanke hulda da kasar Iran wadda ke matsayin babbar abokiyar gabar Saudiyya sai kuma rufe sansanin sojin Turkiyya da ke kasar.

Yayin taron, ministan harkokin wajen saudiyya Adel al-Jubier ya ce matakin da suke kai a yanzu zai ci gaba har zuwa lokacin da Qatar zata martaba bukatun su.

Sai dai kuma a lokacin da ya ke maida martani ministan harkokin wajen Qatar Sheikh Abdurrahman Al-thani ya ce jerin bukatun da kasashen suka mikawa Qatar ba abubuwane masu yiwuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.