Rundunar sojin Iraqi ta ce kiris ya rage ta murkushe IS a Mosul
Wallafawa ranar:
Rundunar sojin kasar Iraqi, ta ce tana ta kwarin gwiwar nan da wasu sa’o’i, zata samu nasarar kwace cikakken iko da birnin Mosul daga hannun mayakan ISIS.
Tun a ranar 17 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, sojin Iraqi tare da hadin gwiwar mayakan Kurdawa na Peshmerga, wadanda jiragen yakin Amurka ke marawa baya, suka kaddamar da farmakin murkushe mayakan ISIS, da suka jima suna iko da birnin na Mosul.
Da fari a watan Janairu da ya gabata rundunar sojin Iraqi ta sanar da karbe ragamar iko da gabashin Mosul, sai dai kuma a bangaren yammacin birnin, rundunar hadin gwiwar ta fuskanci turjiya daga kungiyar ta ISIS.
A baya-bayannan dai majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa, akwai faragabar mayakan na ISIS sun yi garkuwa da akalla fararen hula dubu dari, a cikin birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu