Iraqi

Haidar al-Abadi ya taya sojin Iraqi murna

Firaministan kasar Iraqi, Haidar Albaadi, ya sanar da samun nasarar fatattakar mayakan ISIS daga birnin Mosul da sojin kasar suka yi.

Firaministan Iraqi Haider al-Abadi a lokacin da ya isa birnin Mosul.
Firaministan Iraqi Haider al-Abadi a lokacin da ya isa birnin Mosul. Iraqi Prime Minister Media Office/Handout via REUTERS
Talla

al Abadi, ya sanar da samun nasarar ce a hukumance, a lokacin da ya isa birnin na Mosul a yau Lahadi, domin taya sojin kasar murna bisa gagrumar nasarar da suka samu, bayan da suka kafa tutarsu a kogin Tigris, inda nan ne tunga mafi karfi ta mayakan ISIL, da ke iko da birnin a baya.

Rahotanni sun ce sojin iraqi sun kame ragowar mayakan na ISIS, da sukai kokarin tserewa ta hanyar fadawa kogin na Tigris bayanda sojin Iraqi suka idda murkushe su.

Kubucewar birnin Mosul daga hannun ISIS shi ne rashin nasara mafi girma da kungiyar ta fuskanta, tun bayan mamaye birnin da mayakanta suka yi shekaru uku da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI