Sojin Iraqi sun soma bikin nasara a Mosul
Wallafawa ranar:
Mayakan IS sun lashi takobin ci gaba da yaki har mutuwa a dai-dai lokacin da dakarun Iraqi ke cewa suna gab da kakkabe mayakan baki daya daga birnin a kankanin Lokaci mai zuwa.
Wakilin Kamfanin Dilancin Labaran Reuters, ya rawaito ce tuni dakarun Iraqi suka soma bikin nasara tun kafin a sanar da kwace cikakken ikon Mosul, inda suke amfani da tankokin yaki da bindigu wajen harbe-harben nasara.
Yakin kwato Mosul da aka soma tun a shekarar da ta gabata ya salwantar da duban rayuka, tare da raba miliyoyi da Matsugunai.
Yanzu dai Rahotanni na tabbatar da cewa an karya lagon IS a birnin na karshe da suke da karfi iko ko cibiyarsu a Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu