Iraqi

Iraqi ta kawo karshen ISIL a Mosul

Friministan Iraqi Haidar al-Abadi tare da tawagar sojojin da suka fatataki ISIL a Mosul
Friministan Iraqi Haidar al-Abadi tare da tawagar sojojin da suka fatataki ISIL a Mosul Iraqi Prime Minister Media Office/Handout via REUTERS

A hukumance Friministan Iraqi Haidar al-Abadi ya sanar da nasarar kwato birnin Mosul daga hannu mayakan ISIL a Iraqi, bayan shafe tsawon watanni 9 ana gwabza yaki da mayakan da ke kokarin kafa daularsu a gabas ta tsakiya.

Talla

Al-abadi ya ce dakarun Iraqi sun fatattaki ISIL tare da kame da kamewa bayan shafe tsawon shekaru 3 mayakan na iko da birnin na biyu mafi girma a kasar.

Rashin Mosul da ISIL ta yi babban koma bayane a kokarin da ta ke na mamaye a gabas ta tsakiya.

Rundunar kawance da Amurka ke jagoranta da ta bada gudunmawa a yakin da ake yi a Mosul da Raqa ta bayyana farin cikinta da nasara, sai dai ta gargadi cewar nasaran bai kawo karshan yakin da ta’addanci ba.

Hankula a yanzu sun soma karkata a kan babban aikin da ke akwai nan gaba wajen sake gina birni, da taimakawa fararen hula, yayin da kungiyoyin agaji ke gargadin cewa bukatun tallafin agaji bai kare ba.

Tuni shugaban kasar Amurka Donald Trump da sauran kasashen duniya suka soma aike sakon ta ya murna ga Friminista Haidar al-Abadi na gagarumin nasaran da aka samu kan ISIL a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI