Yemen

Yemen: Annobar kwalara ta shafi mutane dubu 300

Ma'aikatan kwashe shara a birnin Sanaa na Yemen, sun kauracewa aikinsu saboda rashin biyan albashi.
Ma'aikatan kwashe shara a birnin Sanaa na Yemen, sun kauracewa aikinsu saboda rashin biyan albashi. REUTERS/Khaled Abdullah

Kungiyar bayar da agaji ta RedCross ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar Kwalara a Yemen ya kai mutum dubu 300, tun fara gwabza yaki a kasar, wanda ya haddasa yunwa da kuma yawaitar cututtuka.

Talla

A cewar wani kwamitin kungiyar ta RedCross, cutar na ci gaba da yaduwa cikin sauri tun bayan bullarta a watan Afrilun daya gabata.

Robert Mardini daraktan shiyya na kwamitin Redcross, ya ce ana samun sabbin wadanda suka kamu da cutar, kimanin dubu bakwai a kowacce rana a Sanaa, babban birnin Yemen da kuma wasu yankuna uku.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta danganta lamarin da shafe tsawon sama da shekaru uku ana gwabza yaki tsakanin mayakan Houthi na Shi’a da gwamnatin Saudiyya, wanda ya haddasa annobar yunwa sakamakon karancin abinci, dalilin da shi kuma ya kai ga haddasa barkewar kwalara da ta hallaka kimanin mutane dubu daya da dari shida zuwa yanzu.

Jami’in dake kula da harkokin jinkai na majalisar dinkin duniya a Yemen McGoldrick ya ce kimanin mutum milyan 17 na al’ummar Yemen na tsananin bukatar tallafin abinci da sauran kayakin jinkai inda ya ce dole a kara neman wani tallafin kudaden don tafiyar da harkar jinkai a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.