Isra'ila

Dan adam ba zai iya rayuwa ba a zirin gaza a shekara ta 2020

Yankin Gaza
Yankin Gaza MOHAMMED ABED / AFP

Majalisar Dimkin Duniya ta ce yankin Gaza dake ci gaba da fuskantar kawanyar da Israila tayi masa ya zama wani yanki da rayuwa ba zai yiwu ba.Ropert Piper, Babban jami’in hukumar jinkai na Majalisar ya bayyana haka a lokacin da ake gabatar da wani rahoto kan halin da Falasdinawa ke ciki a yankin.

Talla

Jami’in ya ce majalisar ta dade tana hasashen game da matakan na Israila wadanda suka jefa mutanen yankin cikin kuncin rayuwa.

Wani rahotan Majalisar da aka rubuta a shekarar 2012 yace muddin ba’a dauki mataki na kauda kawanyar da Israial ke yiwa Gaza ba, zama a cikin sa ba zai yiwu ba nan da shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI