China

China ta sha suka kan mutuwar Liu Liu Xiaobo

Liu Xiabo, dan kasar China da ya lashe kyautar Nobel ta duniya.
Liu Xiabo, dan kasar China da ya lashe kyautar Nobel ta duniya. Reuters

China ta fuskanci suka daga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama bayan mutuwar Liu Xiaobo a gidan yari duk da ya nemi izninin ficewa kasar domin neman maganin cutar Kansa da ta yi sanadin ajalinsa.

Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da shugabanin kasashen Jamus da Amurka sun bayyana kaduwarsu da mutuwar Liu Xiaobo, dan kasar China da ya lashe kyautar Nobel ta duniya.

Rahotanni daga China sun ce Liu Xiaobo ya rasu ne yana da shekaru 61 sakamakon cutar kansa wadda ta lalata wasu sassan jikinsa, bayan daurin shekaru 11 da aka masa a shekarar 2009 kan laifin tunzira jama’a don kifar da gwamnati.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce mutuwar ta girgiza shi kamar yadda kakakin sa Stepahne Dujjaric ya sanar.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana Liu Xiaobo a matsayin wanda ya dage domin tababtar da ‘yanci.

Sakatare harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya sadaukar da ransa domin ganin kasar ta samu ‘yanci, inda ya bukaci hukumomin China da su saki matarsa da ke tsare.

Hukumar bada kyautar Nobel ta duniya ta ce hukumomin China ke da alhakin mutuwar mamacin.

China da ke shan suka daga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam ta mayar da martani inda ta ce kyautar Nobel da aka ba Liu Xiaobo sabo ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI