Turkiya

Turkiya na bikin zagayowar yunkurin juyin mulki

Dubban 'yan kasar Turkiya da suka yi dafifi don bikin zagayowar ranar da akai yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar.
Dubban 'yan kasar Turkiya da suka yi dafifi don bikin zagayowar ranar da akai yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar. middleeasteye

Dubban ‘yan kasar Turkiya ne suka yi fita zuwa titunan kasar domin bukukuwan zagayowar ranar da aka yi yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba, wanda yayi sanadin hallaka mutane 260 yayinda wasu 2, 196 suka jikkata.

Talla

Mafi akasarin jama’ar da sukai dafifi, sun karkata ne zuwa ga babbar gadar birnin Istanbul, wadda daga nan ne wani sashin rundunar sojin Turkiya suka kaddamar da yukurin juyin mulkin.

A kan gadar ne kuma shugaban kasar Recep tayyib Erdogan ya bayyana alamu na karramawa ga mutane 260 da suka rasa rayukansu, yayinda sukai yunkurin hana sojojin da sukai bore, aiwatar da juyin mulkin.

A lokacin da yake kaddamar da bukukuwan Firaministan kasar Binali Yildrim ya ce za’a cigaba da bukukuwan har zuwa gobe Lahadi.

Tun bayan dakile yunrin juyin mulkin, gwamnatin Erdogan, ta kori sama da ma’aikata dubu 15 cikin harda malaman makaranta, bisa zargin suna da alaka da malamin addini Fethullah Gullen, wanda ake azrgi da kitsa juyin mulkin.

Zalika a gefe guda akalla mutane dubu 50 jami’an tsaron kasar suka kama bisa tuhumarsu da ake, matakin da ‘yan adawa a kasar suke suka da cewa take hakkin dan adam ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.