Turkiya

Erdogan ya sha alwashin dawo da hukuncin kisa

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan. Reuters/Wolfgang Rattay

Bisa dukkanin alamu dangantaka na cigaba da yin tsami, tsakanin kasar Turkiya da kungiyar tarayyar turai EU, bayanda a yau shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin maido da hukuncin kisa, karkashin dokar kasar, tare da cewa zasu raba gari da kungiyar ta EU.

Talla

Shugaban ya kuma zargin kungiyar ta EU da jan kafa wajen bai wa Turkiya damar shiga cikinta, bayan shafe shekara da shekaru tana fafutukar gannin bukatar ta tabbata, duk kuwa da jerin sharuddan da ta gindayawa kasar wadda kuma ta cika.

Erdogan ya bayyana haka ne yayinda yake gabatar da jawabinsa na karshe ga al’ummar kasar, da ke gudanar da bikin zagayowar ranar da akai yukurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.

Akalla ma’aikata dubu 150, 000, gwamnatin Erdogan ta kora, yayinda aka kama wasu dubu 50,000 bisa zargin suna da alaka da yukurin juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI