Isra'ila

Hukumomin Isra'ila sun sake bude Masallacin Al-Aqsa

Hukumomin Isra’ila sun bude Masallacin al-Aqsa da ke birnin Jerusalem, bayan rufe da suka yi tsawon kwanaki 2, domin tabbatar da tsaro a harabarsa, biyo bayan musayar wuta tsakanin wasu Falasdinawa uku da jami’an tsaron Isra’ila.

Falasinawa Musulmi da suka kauracewa shiga Masallacin Al-Aqsa sakamakon sabbin matakan tsaron da aka kafa a kofar shigarsa
Falasinawa Musulmi da suka kauracewa shiga Masallacin Al-Aqsa sakamakon sabbin matakan tsaron da aka kafa a kofar shigarsa presstv
Talla

A ranar juma’ar da ta gabata ne falasdinawan suka harbe wasu ‘yan sanda Israila biyu a cikin tsohon birnin Jerusalem, inda suka tsere zuwa Masallacin na al-Aqsa, inda a nan ne ‘yan sandan Isra’ila suka hallaka su.

To sai dai bayan bude Masallacin da aka yi, a yau Lahadi, Falasdinawa sun ki shiga domin gudanar da ibada, saboda na’urorin bincike da aka kafa a kofar shigarsa, hakan yasa suka gudanar da ibada, a wajen Masallacin.

A cewar Sheikh Omar Kiswani, mai magana da yawun wadanda suka kauracewa shiga Masallacin, basu amince da matakin hukumomin tsaron Isra’ilan ba na kafa na’urorin gano karafuna da kuma Karin na’urorin daukar hoto da aka kafa a dukkanin kofofin shiga Masallacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI