Philippines

Anyi kokarin kashe Shugaban kasar Philippines

Hukumomin Kasar Philippines sun ce an raunana masu tsaron shugaban kasar Rodrigo Duterte lokacin da aka budewa tawagar motocin su wuta kwana guda bayan yan tawayen kasar sun sanar da shirin kaddamar da sabbin hare hare.

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte Handout / PRESIDENTIAL PHOTO DIVISION / AFP
Talla

Birgediya Janar Gilberto Gapay dake yankin Mindanao yace shugaba Duterte bayan cikin tawagar motocin lokacin da aka kai harin.

Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban kasar ya bukaci Majalisar kasar ta amince da barin yankin a karkashin dokar ta baci har sai an murkushe masu tada kayar baya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI