Falasdinu

"Ya kamata ICC ta kawo karshen bincikenta a yankunan Falasdinawa"

Yakin Isra’ila da Hamas a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 2, 000 da suka hada da yara 551.
Yakin Isra’ila da Hamas a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 2, 000 da suka hada da yara 551. AFP PHOTO / THOMAS COEX

Kungiyoyin fararen hula da lauyoyi a yankunan Falasdinawa sun bukaci kotun duniya ta ICC ta gaggauta kammala binciken da ta ke yi game da laifukan yaki da aka aikata a Gaza da gabar yamma da kogin Jordan da gabashin birnin Kudus.

Talla

Falasdinawan sun ce shekaru biyu da aka shafe kotun na bincike ya dace ace ta kammala binciken ta’asar da Isra’ila ta aikata a yakin da aka yi a Gaza a 2014.

Lauyoyin da suka yi kiran ga Kotun ICC na wakilatar Falasdinawa 448 da yakin Gaza ya shafa.

Sannan akwai kungiyoyin fararen hula sama da 50 na Falasdinawa da suka bukaci kotun ICC ta gaggauta kammala bincikenta akan laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a yaki tsakaninta da Hamas a 2014

lauyoyin sun ce shekaru biyu sun isa ace kotun ICC ta gano wani abu a binciken da ta kaddamar a 2015 a yankunan na Falasdinawa.

A watan janairun 2015 ne kotun ta kaddamar da bincike akan laifukan yaki da aka aikata daga bangaren Isra’ila da Hamas a yakin Gaza wanda ya kashe Falasdinawa sama da 2, 000 da suka hada da yara 551.

Wannan ne karon farko da Kungiyoyin fararen hular da suka hada da likitoci da manoma da malamai suka shigar da kokensu ga kotun ta ICC.

Kuma sun ce sun dauki matakin ne saboda sun lura akwai gazawa daga bangaren gwamnatin Falasdinawa game da gaggauta binciken na ICC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.