Thailand

Kotun Thailand ta daure Janar na soji kan safarar baki

An yankewa Laftanar Janar Manas Kongpan hukuncin zaman gidan yarin shekaru 27 kan safarar bakin-haure
An yankewa Laftanar Janar Manas Kongpan hukuncin zaman gidan yarin shekaru 27 kan safarar bakin-haure REUTERS/Athit Perawongmetha/File Photo

Wata Kotu a kasar Thailand ta daure wasu mutane 62 a gidan yari saboda samun su da hannu wajen laifin safarar baki ‘yan kabilar Rohingya da kuma ‘yan kasar Bangladesh, cikin su harda wani Janar na sojin kasar.

Talla

Hukuncin kotun ya biyo bayan kaddamar da wani samame da hukumomin kasar Thailand suka yi a shekarar 2015, kan wata kungiya da ta shafi jami’an gwamnati da ‘yan banga da ke tara miliyoyin kudade wajen taimakawa baki ‘yan kasashen waje da ke neman shiga kasar, yayin da suke garkuwa da wasu har sai sun biya diyya.

Cikin wadanda aka daure harda wani Laftanar Janar Manas Kongpan na rundunar sojin kasar, wanda kotun ta daure shekaru 27 a gidan yari.

Alkalin kotun ya ce Janar din na da hannu wajen aikata manyan laifukan da suka shafi kasa da kasa da kuma taimakawa masu safarar baki.

Sauran sun hada da wani dan kasar Myanmar da aka samu da hannu, wanda aka daure shekaru 94 a gidan yari da kuma wasu 17 da aka daure sama da shekaru 70.

A karkashin dokar Thailand, dan fursina ba ya wuce shekaru 50 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.