Israel-Palestine

An tsaurara matakan tsaro a zagayen masallacin Quds

Masu ibada a masallacin Quds
Masu ibada a masallacin Quds REUTERS/Ammar Awad

Rundunar sojin Isra’ila ta tsaurara matakan tsaro kusa da Masallachin Al’Aqsa da ke birnin Quds domin magance fushin Falasdinawan da za su halarci sallar Juma’a a yau, sakamakon sabbin matakan da mahukuntan Isra’ilar suka dauka domin hana wani rukuni na jama’a zuwa kusa da masallancin.

Talla

An dai share tsawon kwanaki ana zaman dar dar, sakamakon matakin rufe masallancin da Isra’ila ta dauka, yayin da a wannan juma’a ta ce mata da kuma maza wadanda shekarunsu suka wuce 50 kawai ne za a bai wa damar shiga masallancin domin yin sallah a cikinsa.

Kasashen duniya da dama ne suka yi suka dangane da wannan mataki, wanda ya haifar da tashe-tashen hankula musamman daga bangaren Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI