Israel-Palestine

Abbas ya katse duk wata hulda da Isra'ila

Farfajiyar masallacin Quds
Farfajiyar masallacin Quds AFP/Abbas Momani

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanar da katse duk wata hulda ko kuma tattaunawa da mahukuntan Isra’ila, sakamakon matakan da suka dauka na hana jama’a isa ga masallacin Quds domin gudanar da ibada, lamarin da ya yi sanadiyyar barkewar tarzoma har ma da samun asarar rayuka.

Talla

Abbas ya bayyana cewa dole ne Isra’ila ta janye daruruwan jami’an tsaron da ta jibge a zagayen masallacin, tare da bai wa jama’a damar isa domin gudanar da ibada.

A jiya juma’a, artabun da aka yi tsakanin falasdinawa da jami’an tsaron na Isra’ila, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane6, uku Falasdinawa da kuma wasu yahudawa uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.