Qatar-Saudiya

Saudiya na zargin kungiyoyin agaji da hannu a ta'addanci

Taron kasashen larabawa dangane da batun rikicin Qatar
Taron kasashen larabawa dangane da batun rikicin Qatar REUTERS/Khaled Elfiqi

Saudi Arabia da kawayen ta sun bayyana wasu kungiyoyin agaji a kasashen Yemen da Qatar da Libya a matsayin kungiyoyin yan ta’adda saboda abinda suka kira alakar su da masu ayyukan ta’addanci.

Talla

Sanarwar da Saudiya da Daular Larabawa da Bahrain da kuma Masar suka bayar ta hadin gwuiwa ta bayyana kungiyoyin guda tara da kuma wasu mutane 9 da suka ce suna alaka da Gwamnatin Qatar a matsayin yan ta’adda.

Tuni kasashen 4 suka gabatar da bukatu 13 da suke neman ganin Qatar ta aiwatar cikin su harda rufe tashar Al Jazeera kafin cire mata takunkumin da suka kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.