Taliban ta kashe sojojin Afghanistan 26
Wallafawa ranar:
Akalla sojojin Afghanistan 26 sun rasa rayukansu a wani kazamin hari da kungiyar Taliban ta kaddamar musu a sansaninsu da ke kudancin birnin Kandahar, yayin da a bangare guda, sojojin suka yi nasarar hallaka mayaka 80.
Sojin sama na Afghanistan sun taimaka wa sojin kasa a yayin gwabzawar da aka yi ta kusan yini biyu da Mayakan Taliban.
Baya ga sojoji 26 da suka mutu a harin, an kuma samu 13 da suka jikkata kamar yadda Janar Dawlat Waziri, mai magana da yawun sojin ya sanar.
Mr. Dawlat ya tabbatar cewa, mayakan Taliban kimanin 80 suka mutu a yayin fafatawar, wadda ta kawo karshe a safiyar yau Laraba.
Kwamandan sojin sama a Lardin Kandahar, Janar Raziq Shirzai, ya ce, sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen yi wa Mayakan Taliban lugudun wuta.
Sai dai har yanzu, akwai sojoji 12 da ba a ji duriyarsu ba tun bayan lafawar gunmurzun, wanda jami’an tsaron kasar suka bayyana a matsayin gagarumi.
Rahotanni sun ce, Mayakan sun yi nasarar kwashe wasu makamai gabanin fatattakarsu baki daya.
Mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce, kimnanin motoci 30 ne jere da juna da ke dauke da daruruwan Mayakan Taliban suka kai harin kan sansanin sojin.
Taliban dai ta dauki alhakin harin ne ta hanyar kafar sada zumnunta ta Twitter.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu