Pakistan
Kotun koli ta hana wa Firaminista Nawaz Sharif rike duk wani mukami
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotun kolin Pakistan ta yanke hukuncin da ke haramta wa Firaministan kasar Nawaz Sharif rike duk wani mukami, bayan samun sa da laifin rashawa.
Talla
Kotun ta gudanar da bincike ne a game da zargin rashawa da kuma mallakar dukiya a kasashen ketare da ake yi wa firaministan, bayan da rahoton tonon silili na Panama Papers ya ambato cewa Sharif ya mallaki dimbin dukiya a ketare.
Hukuncin dai na nufin cewa dole ne Nawaz Sharif ya sauka daga mukaminsa sannan kuma ya fuskantar shara’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu