Saudi

Saudiya ta kakkabo makami mai linzami kusa da Makkah

Yariman Saudiya mai jiran gado kuma ministan cikin gida Mohammed Bin Nayef
Yariman Saudiya mai jiran gado kuma ministan cikin gida Mohammed Bin Nayef REUTERS

Saudi Arebiya ta yi nasarar harbo wani babban makami mai linzami da mayakan Huthi suka cilla kusa da birnin Makkah a daren Alhamis. Wannan na zuwa a yayin da kasar ke shirye shirye soma gudanar aikin hajjin bana.

Talla

Sanarwar da Saudiya da kawayenta suka fitar da ke yakar ‘yan tawayen Huthi a Yemen, sun ce an yi nasarar harbo makamin ne a tsakanin tazarar kilomita 69 da birnin Makka da ke yammacin kasar.

Kuma sanarwar ta kara da cewa mayakan Huthi ‘yan shi’a na kokarin dagula ayyukan hajji ne a bana da za a fara a watan Agusta.

Mayakan Huthi dai sun dade suna cilla makami mai linzami mai cin gajeren zango a kudancin Saudiya da ke kan iyaka da Yemen wanda ya nuna alamun suna kokarin kai hari ne a Makkah.

A watan Oktoba saudiya ta taba kakkabo wani babban makami mai cin dogon zango da mayakan na Huthi suka cilla kusa da garin Makkah.

Sabon harin na yanzu kuma na a matsayin barazana ga aikin hajji, inda mutane sama da miliyan biyu ke taruwa domin ibada a birnin Makkah.

Yakin Yemen dai ya kashe mutane sama da 8,000 tare da jikkata sama da 44,000 tun lokacin da Saudiya da kawayenta suka abkawa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI