Qatar

Kasashen Larabawa na kan bakarsu game da Qatar

Ministocin Kasashen Larabawa a Bahrain, in da suka gudanar da taro kan Qatar
Ministocin Kasashen Larabawa a Bahrain, in da suka gudanar da taro kan Qatar REUTERS/Hamad I Mohammed

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa da suka yanke huldar Diflomasiya da Qatar sun ce, a shirye suke su tattauna da ita, muddin Qatar din za ta mutunta sharuddan da aka gindaya ma ta, kuma sun ce, suna kan bakarsu don ganin ta sauya manufofinta.

Talla

Tun a ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata ne, kasashen Larabawan da suka hada da Saudiya da Bahrain da Masar da Daular Larabawa suka katse hulda da Qatar bisa zargin ta da tallafa wa ‘yan ta’adda, zargin da Qatar ta sha musantawa.

A wata ganawa da suka yi a yammacin jiya Lahadi, Ministocin Harkokin Wajen , sun ce, a shirye suke su tattauna da Qatar amma akan sharadin cewa, za ta dakatar da bai wa ‘yan ta’adda tallafi.

Ministocin sun kara da cewa, suna nan kan bakarsu ta ganin cewa Qatar ta mutunta sharudda 13 da aka gindaya ma ta kafin janye takunkumin da kasashen suka kakaba ma ta.

Daga cikin sharuddan dai, akwai batun rufe kafar talabijin ta Al-Jazeera, da rufe sansanin sojin Turkiyya da ke Qatar baya ga gurgunta huldarta da Iran.

Tuni kasashen na Larabawa suka janye jakadunsu daga birnin Doha, sannan kuma sun umarci dukkanin ‘yan asalin Qatar da su koma kasarsu.

Har ila yau, kasashen karkashin jagoranci Saudiya sun haramta wa Qatar keta sararin samaniyarsu.

Kasar Qatar ta yi watsi da dukkanin sharuddan tare da zargin Saudiya da yunkurin hana ‘yan kasarta zuwa aikin hajjin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI