India

Kotu ta kashe aure saboda rashin makewayi

Kotu a India ta ba iwa wata mata umurnin rabuwa da mijin ta saboda gaza samar mata da makewayi a gidan da suke. Rahotanni sun ce akalla mutane miliyan 600 ke bayan gida a filin Allah a kasar saboda rashin gina ban daki a gidajen su.

Kotun Kolin kasar India
Kotun Kolin kasar India Reuters
Talla

Alkalin kotun Rajendra Kumar Sharma da ke Jihar Rajasthan ya amince da karar da matar ta shigar inda take cewar rashin samar mata da ban daki a gidan su bayan shekaru 5 da yin aure ya zama mugunta.

Alkali Sharma yace abin takaici ne yadda ake sanya mata a kauyukan India ke jiran sai dare yayi su tafi daji domin biyan bukatun su, saboda haka ya raba auran.

Wannan dai ba shine karo na farko da ake raba aure saboda rashin ban daki ba.

Hukumar UNICEF tace mutane miliyan 600 a India, wanda shine rabin al’ummar kasar, ke bayan gida a filin Allah.

Firaminista Narendra Modi yayi alkawarin gina ban daki a kowanne gida nan da shekara ta 2019 domin shawo kan matsalar, kuma tuni ya gina miliyan 20 yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI