Isa ga babban shafi
China

China ta tsaurara sharuddan amfani da shafukan Intanet

Babban Shafin sadarwa na  Weibo a China
Babban Shafin sadarwa na Weibo a China Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Gwamnatin China ta bukaci kamfanonin sadarwa na intanet a kasar su dinga tantance masu mu’amula da su kafin ba su damar wallafa wani bayani a shafukan. Wannan wani mataki ne da ake ganin China ta duka na tsaurara matakan amfani da intanet.

Talla

Ofishin da ke kula da intanet ya bukaci kamfanonin saarwar su tantance asalin mutum kafin ya wallafa wani batu ko kuma yin tsokaci.

Sannan China ta tilaswa kamfanoni su goge duk wani batu da aka wallafa da ya saba ka’ida tare da sanar da hukumomi.

A ranar 1 ga Oktoba matakin zai soma aiki a China.

Za a bukaci masu amfani da shafukan na intanet su dauki hoton kwafi na katinsu na shaida, domin tabbatar da asalin mai amfani da shafin, matakin da ya janyo suka daga ‘yan rajin kare hakkin dan adam.

Karkashin tsarin yana da wahala a wallafa batu ta hanyar boye suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.