Falasdinu

Guterres na ziyarar farko a yankin Falasdinu

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yana gaisawa da shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin yayin tattaunawar da suka yi a Jerusalem, 28 ga Agustan 2017.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yana gaisawa da shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin yayin tattaunawar da suka yi a Jerusalem, 28 ga Agustan 2017. REUTERS/Ronen Zvulun

Babban magatakatardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, a wannan litinin yana gudanar da ziyarar aiki a yankin Gabas ta Tsakiya, karo na farko tun bayan darewarsa kan mukamin.

Talla

Da farko dai Guterres zai gana da firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu, daga bisani kuma ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, domin jagorantar cigaba da kokarin kawo karshen rikicin da aka shafe akalla shekaru 70 ana yi tsakanin bangarorin biyu.

Jakadan yankin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya ce ziyarar magatakardan ta zo ne a lokacin da ake bukatarta, domin karfafa yunkurin da ake na samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu.

Kasar Amurka da Isra’ila dai sun sha zargin Majalisar Dinkin Duniya da karkata zuwa bangaren Falasdinawa, musamman kan takaddamar cigaba da mamayar yankin zirin gaza da gina Karin gidaje don tsugunnar da Yahudawan a yankin Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.