Malaysia

Gobara ta kashe daliban Islamiyya 22 a Malaysia

Makarantar Darul Quran Ittifaqiyyah, in da dalibai suka rasa rayukansu a wata gobara
Makarantar Darul Quran Ittifaqiyyah, in da dalibai suka rasa rayukansu a wata gobara REUTERS

Akalla daliban wata makarantar Islamiyya 22 da suka hada da malamai biyu sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a dakin kwanansu da ke tsakiyar birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Talla

Rahotanni sun ce, masu aikin kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar wadda ta tashi da safiyar yau a Darul Quran Ittifaqiyyah, in da dalibai ke haddar Al-Kur'ani, yayin da hukumomin kasar suka bayyana gobarar a matsayin mafi muni da aka gani cikin shekaru 20.

Gabalin mutuwarsu, Daliban sun yi ta kwala ihu, suna neman taimakon jama’a, amma babu wanda ya kai dauki a wannan lokaci saboda munin gobarar.

Akasarin Daliban na tsakanin shakara 13 zuwa 17 da haihuwa kuma dukkaninsu maza ne

Ministan ilimi Tengku Adnan Tengku Mansor ya ce, rashin hanyoyin fita daga dakin kwanan daliban ya taimaka wajen mutuwarsu.

Shugaban 'yan sandan birnin Kuala Lampur, Amar Singh ya ce, sun samu gawarwakin daliban menne da juna, kuma alamu sun nuna cewa, sai da aka samu turmutsisi kafin mutuwarsu.

Dalibai 14 sun samu nasarar tsira da rayukansu bayan tashin gobarar ta hanyar durowa ta taga, yayin da wasu kuma ke kwance a asibiti.

Hukumomin kasar sun ce, ana gudanar da makarantar ce ba tare da cikakken lasisi daga gwamnatin kasar ba, kuma tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda mataimakin Firaminista Ahmad Zahid Hamidi ya bayyana.

Kashi 60 na al'ummar Malaysia mai yawan mutane miliyan 30 Musulmai ne

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.