Syria

Sojin saman Isra'ila sun kai hari kusa da birnin Damascus

Hoton da tauraron dan adam na Isra'ila ya dauko, wanda ga alama wata cibiyar kera makamai masu linzame ne mallakin Iran a gabashin Syria.
Hoton da tauraron dan adam na Isra'ila ya dauko, wanda ga alama wata cibiyar kera makamai masu linzame ne mallakin Iran a gabashin Syria. ©IMAGESAT INTERNATIONAL N.V./Handout via REUTERS

Jiragen yakin Isra’ila sun kai farmaki ta sama a kan wani wuri da kasar ta ce rumbun ajiye makamai ne a kusa da birnin Damascus na Syria.

Talla

Isra’ial ta ce rumbun ajiye makaman mallakin kungiyar Hezbollah ce ta kasar Lebanon, kuma wannan shi ne dalilan kai hari domin lalata makaman.

Ba wannan ne karo farko da Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a cikin kasar ta Syria ba a ‘yan makonnin baya-bayan nan, matakin da Syria ta bayyana shi da cewa tsokana ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.