Isra'ila

Isra'ila ta musanta zargin kutse a zaben raba gardamar Kurdawan Iraqi

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Reuters

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya musanta zargin da Turkiyya ta wa kasar sa na yin kutse a zaben raba gardamar Kurdawa a Iraqi. Isra’ila dai na daga cikin kasashen da ke goyon bayan ballewar Kurdawa daga Iraqi.

Talla

A jiya Asabar ne shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce hukumar leken asrin Isra’ila ta taka rawa a zaben raba gaedamar yankin Kurdawa na ranar 25 ga Satumban daya gabata, ganin yadda Kurdawan suka rika daga tutar Isra’ila yayin bukukuwan murnar nasarar da suka samu.

A cewar Netanyahu, tabbas Isra’ila na goyon bayan samun ‘yancin yankin amma bata taka rawa a zaben raba gardamar kamar yadda Turkiyya ke zargi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.