Iraqi-Iran

Rundunonin sojin Iran da Iraqi zasu yi atasayen hadin gwiwa

Wasu Kurdawa da ke goyon bayan ballewar yankinsu daga Iraqi.
Wasu Kurdawa da ke goyon bayan ballewar yankinsu daga Iraqi. REUTERS/Ako Rasheed

Kasashen Iran da Iraqi sun ce rundunonin sojinsu, zasu yi atasayen hadin gwiwa a mashigai da dama da ke kan iyakar Iran da yankin Kurdawa na Iraqi, wato Kurdistan.

Talla

Sanar da shirin fara atasayen, ya zo ne bayanda kusan kashi 93 daga cikin al’ummar Kurdawan suka kada kuri’ar goyon bayan ballewar yankin daga kasar Iraqi, a zaben raba gardamar da suka yi a farkon makon da ya gabata, wanda gwamnatin kasar ta ce haramtacce ne.

Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da Sojojin Iraqi suka gudanar da atasayen hadin gwiwa da sojin Turkiya duk dai a gaf da kan iyakar kasar da yankin Kurdawan, a wani mataki na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Iraqi ta bada umarni dakatar da sauka da tashin jiragen sama a birnin Erbil na yankin Kurdawa, wanda ke a matsayin martani ga zaben raba gardamar ballewa daga kasar da Kurdawan suka kada.

Hukumomin Bagadaza sun ce za su ci gaba da matsin lambar tabbatar da cewa Kurdawan sun mika kai.

Dakatar da sufurin jiragen sama a yankin Erbil, shi ne takukumin farko da gwamnatin Bagadaza ta kakabawa kurdawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.