Indonesia

Yawan wadanda suka tserewa dutse mai aman wuta ya wuce kima

Tsaunin Agung na tsibirin Bali, da ke barazanar fara aman wuta da kuma narkakken dutse a kowane lokaci.
Tsaunin Agung na tsibirin Bali, da ke barazanar fara aman wuta da kuma narkakken dutse a kowane lokaci. AFP

Gwamnan tsibirin Bali na kasar Indonesia, da ke amsa sunan I Made Mangku Pastika, ya ce yawan mutanen da suka tsere daga gidanjensu a dalilin fargabar aman wutar da tsaunin Agung ka iya a kowane lokaci ya wuce kima.

Talla

A cewar Gwamna Pastika, jama’ar da suke wajen da’ira, ko murabba’in kilomita 12 daga tsaunin su koma gida, saboda gujewa zama matsala da nauyi ga jami’an bada agajin da ke lura da wadanda hukumomi suka tilastawa ficewa daga gidanjensu

Sama da mutane 145,000 suke tsere daga gidajensu a tsibirin na, don gujewa aman wuta da narkakken dutsen da tsaunin na Agungu ke barazanar yi a kowane lokaci, bayan wanda yayi a 1963.

A halin da ake ciki sansanin da aka tanadarwa mutane dubu 70,000 da suke fice daga da'ira, ko murabba'in kilomita 12 da aman wutar ka iya shafa, yayi cikar kwari da sama da mutane 140,000, abinda ke barazanar haifar da babbar matsala ga ayyukan jami'an agaji.

A shekara ta 1963 aman wutar tsaunin yayi sanadin mutuwar sama da mutane 1,600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.