Somalia

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutum 30 a Somalia

Ana fargabar karuwar adadin wadanda suka mutu a tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai yau birnin Mogadishu na Somalia.
Ana fargabar karuwar adadin wadanda suka mutu a tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai yau birnin Mogadishu na Somalia. REUTERS/Feisal Omar

Akalla mutane 30 ake fargabar sun mutu sanadiyyar wasu tagwayen hare-haren kunar bakin da 'yan bindiga suka kai da mota gab da wani Otel a Magadishu babban birnin Somalia a yau Asabar.Haka zalika akwai fargabar karuwan adadin wadanda suka mutun, la'akari da yadda mutane da dama suka samu munanan raunuka.

Talla

Harin wanda ya faru a tsakiyar birnin a dai dai yankin da aka kebe don ofisoshi da ma’aikatun gwamnatin kasar, haka zalika wajen da ake da yawan jama’ar da ke kai da komo ya ruguje gine-gine da dama baya ga dubban ababen hawan da suka kone.

Wani jami’in tsaro Abdullahi Nur ya shaidawa Reuters cewa kawo yanzu ba a kai ga gano adadin mutanen da suka jikkata sanadiyyar harin ba, haka zalika adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa a kowanne lokaci.

Har yanzu dai babu kungiyar da ta dau alhakin harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.