Syria

Fararen hula dubu 3 sun fice daga Raqqa a Syria

Kakakin sojin Syria ya ce yanzu haka mayakan IS na kasar suma sun fice daga birnin na Raqqa da iyalansu baki daya.
Kakakin sojin Syria ya ce yanzu haka mayakan IS na kasar suma sun fice daga birnin na Raqqa da iyalansu baki daya. REUTERS

Sama da fararen hula dubu 3 ne suka bar birnin Raqqa na Syria daga daren jiya zuwa yau karkashin yarjejeniyar da aka kulla don komawa yankunan da Sojin Syria ke iko da su.Kawo yanzu dai birnin zai rage sai iya mayakan kungiyoyin jihadi na kasashe ne da suka ki amincewa da kulla yarjejeniya tun da farko da yawansu bai gaza mutum dari 3 zuwa 4 ba.

Talla

Kakakin sojin Syria ya ce yanzu haka mayakan IS na kasar suma sun fice daga birnin na Raqqa da iyalansu baki daya.

Wata sanarwa da Sojin suka fitar yau ta ce bata amince koda guda cikin mayakan jihadin kasashen wajen su bar yankin na Raqqa ba.

A bangare guda kuma Turkiyya ta yi watsi da bukatar Syria dangane da janye dakarun sojinta daga arewa maso yammacin Idlib.

Wani babban jami’in gwamnatin Turkiyyar ya ce bukatar bata yi dai dai da muradin al’ummar yankin ba, inda ya ce Syrian ba ta bayar da wata hujjar bukatar hakan ba.

Ko da yake da Ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa ci gaba da zaman dakarun na Turkiyya a yankin Idlib ya sabawa dokar kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.