Myanmar

Kananan yara dubu 14 aka hallakawa iyaye a Myanmar

A kowacce rana adadin Musulmi 'yan kabilar Rohingya da ke kwararowa zuwa Bangaladesh na karuwa, a dai dai lokacin da rikici ke kara tsananta a Myanmar.
A kowacce rana adadin Musulmi 'yan kabilar Rohingya da ke kwararowa zuwa Bangaladesh na karuwa, a dai dai lokacin da rikici ke kara tsananta a Myanmar. Reuters

Jami'an da ke kula da musulmi 'yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a Bangaladesh  sun ce sun gano akalla kananan yara dubu 14 cikin 'yan gudun hijirar wadanda aka kashe musu iyaye yayin tsallakowa Kasar daga Myanmar.

Talla

Sanarwar na zuwa ne a dai dai lokacin da majalisar dinkin duniya cewa adadin musulmai ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere daga Myanmar ya kai mutum dubu dari biyar da 36 cikin kasa da watanni uku, inda tace hakan alamu ne na yunkurin shafe kabilar ta Rohingya.

Jami’an agajin Bangaladesh sun bayyana cewa da dama daga cikin yaran an tsince su ne akan iyakar kasar da Mynamar yayinda wasu da dama suka rasa mahaifansu a kan hanyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.