Iraqi

Dakarun Iraqi sun shiga Kirkuk

Dakarun Iraqi sun shiga Kirkuk domin kakkabe mayakan Kurdawa
Dakarun Iraqi sun shiga Kirkuk domin kakkabe mayakan Kurdawa REUTERS

Dakarun Iraqi sun sanar da kwato wasu muhimman wurare da suka hada da ofishin gwamnan lardin, a yayin da suke kokarin kwato garin Kirkuk daga hannun mayakan Kurdawa.

Talla

Daruruwan mutane ne suka fice daga garin na Kirkuk bayan dakarun Iraqi sun kaddamar da yakin kakkabe mayakan Kurdawa daga yankin.

Iraqi na dab da kwace garin Kirkuk bayan sun kwato ofishin gwamnan lardin da sansanin soji da cibiyoyin mai da kuma tashar jirgin sama.

Dakarun na Iraqi sun shiga Kirkuk ne da tankokin yaki domin kwato birnin da mayakan kurdawa suka kwace daga hannun mayakan IS.

Dubban mazauna Kirkuk ne suka fice bayan dakarun Iraqi sun kaddamar da yakin kwato garin inda rahotanni suka ce hanyoyi sun toshe musamman wadanda ke zuwa yankin arewacin Iraqi saboda yawan mutanen da ke ficewa.

Yunkurin kwato garin dai na dada haifar da fargaba kan yiyuwar ballewar yaki tsakanin gwamnatin Iraqi da kuma kurdawan da suka jefa kuri’ar ballewa daga kasar.

Rundunar kawance ta kasashen yammaci da Amurka ke jagoranta sun bukaci bangarorin biyu su mayar da hankali ga yakar ta’addancin IS maimakon yakar juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.