China

Taron Jamiyyar Kwaminisanci karo na 19 a China

Shugaba Xi Jinping na China a taron Jamiyyar Kwaminisanci da aka fara gudanarwa yau a kasar.
Shugaba Xi Jinping na China a taron Jamiyyar Kwaminisanci da aka fara gudanarwa yau a kasar. REUTERS/Jason Lee

A yayin bude babban taron jam’iyyar kwaminisanci a China, Shugaban kasar Xi Jinping ya ce China za ta ci gaba da bude kofofinta ga kasashen duniya domin zuba jari da kuma gudanar da harkokin kasuwanci. Taron jam’iyyar shi ne karo na 19 wanda zai tabbatar da makomar shugabancin China.

Talla

Bayan kowanne shekaru 5 ne ake gudanar da babban taron jam’iyyar kwaminisancin na China wanda kuma za a shafe tsawon mako guda ana gudanarwa.

Wakilan Jam’iyar kwaminisancin mai mulkin China sama da 2,000 suka halarci taron wanda zai tantance jagora da kuma alkiblar kasar..

Ana sa ran taron ya sake ba shugaba Xi jinping sabon wa’adin shugabanci na shekaru 5 kuma a matsayin jagoran jam’iyyar.

Sannan a taron za a zabi sabbin mambobin babban kwamitin da zai jagoranci lamurran kasar da zai kunshi shugaban kasa da mataimakinsa.

A cikin jawabinsa na bude taron shugaba Xi y ace China za ta ci gaba da bude kafofin tattalin arzikin ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.