Bakonmu a Yau

AbdulKadir Muhammad kan shirin gwamnatin Saudiya na shawo kan matsalar tsattsauran ra'ayi

Sauti 03:35
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul Aziz.
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul Aziz. REUTERS/Lintao Zhang/Pool/Files

Gwamnatin Saudi Arabia na shirin kafa wata Majalisa da zata yi nazarin wasu litattafan da ake zargin wasu Malamai na amfani da su wajen sanyawa mabiyansu tsatsauran ra’ayi. Sarki Salman Bin Abdul Aziz yace Majalisar wadda zata janyo masana daga sassan duniya, zata gudanar da ayyukan ta a kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulqadir Muhamamd Suleiman na Jami’ar Abuja dangane da tasirin wannan mataki.