Afghanistan

Harin kunar bakin wake ya hallaka sojin Afghanistan 43

Hoton harin da mayakan Taliban suka kai kan sansanin sojin Afghanistan da ke yankin Maiwand na lardin Kandahar.
Hoton harin da mayakan Taliban suka kai kan sansanin sojin Afghanistan da ke yankin Maiwand na lardin Kandahar. REUTERS/Stringer

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da sanyin safiyar yau a sansanin soji da ke yankin Maiwand na lardin Kandahar, ya hallaka sojin Afghanistan 43, tare da raunata wasu guda 9, yayinda har yanzu ba'a gano wasu jami'an sojin kasar 6 ba.

Talla

Ma'aikatar tsaron kasar ta kara da cewa sojoji 2 ne kawai suka tsira ba tare da samun rauni ba, yayinda sojojin suka samu nasarar hallaka mayakan Taliban 10.

Harin dai shi ne irinsa na uku da kungiyar Taliban ke daukar alhakin kai wa kan sojin Afghanistan a cikin mako guda, hakan yasa jimillar jami’an tsaro da fararen hular da mayakan na Taliban suka hallaka a baya bayannan ya haura 100.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar ta Afghanistan Dawlat Waziri ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa mayakan sun kaddamar da harin ne ta hanyar tarwatsa bama baman da ke makare wata mota da suka yi kokarin kutsawa da ita cikin sansanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.