Afghanistan

An kai hare hare a Masallatai a Afghanistan

Jami'an tsaro sun kewaye masallacin da aka kai hari a Kabul
Jami'an tsaro sun kewaye masallacin da aka kai hari a Kabul REUTERS/Omar Sobhani

Kungiyar Isis ta dau alhakin harin kunar bakin waken da aka kai jiya juma’a kan masalacin yan shi’a dake birnin Kabul na kasar Afghanistan, inda mutane 39 suka rasa rayukansu, kanar yadda kungiyar ta Isis ta sanar a yau assabar.A wani sako da ta yada a shafin Telegram, Isis ta bayyana dan kunar bakin waken da ya kai harin da sunan Abu Umar, dan Turkmen da cewa ya yi nasarar yin shahada ne, ta hanyar tada bamabaman da ya yi Falmara da su, a masalacin juma’ar dake cike da mabiya mazahabar Shi’a dake Kabul babban birnin kasar Afghanistan.

Talla

A jiya Kakakin rundunar ‘yan sandan Kabul Abdul Basir Mujahid ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa an kai hare-haren ne sau biyu.

Na farko an kais hi ne kan masallacin mabiya mazhabar shi’a inda aka hallaka mutane 39 cikin harda mata da kananan yara, sai kuma wasu 45 da suka jikkata.

Hari na biyu kuwa an kai shi ne kan masallacin Sunni inda mutane 20 suka hallaka sai wasu 10 da suka jikkata.

Gwamnan Yankin Mohsen Danishyar yace an kai harin ne domin hallaka wani kwamandan Yan Sanda kuma harin ya ritsa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.